Revelation 2:1 — Compare Translations
3 translations compared side by side
Hausa (Sabon Rai Don Kowa 2020)
“Zuwa ga mala’ikan ikkilisiya a Afisa, ka rubuta, Waɗannan su ne kalmomi na wannan wanda yake riƙe da taurari bakwai a hannunsa na dama yana kuma tafiya a tsakanin alkukan fitilu bakwai na zinariya.
Hausa Arabic 2020 (أَتَّوْرَتْ دَ أَنَّبَاوَا)
«رُبُوتَ وَمَلاَىِٕكَنْ جَمَعَرْ مَاسُبِے أَعَڢِسَ ثٜىٰوَ «غَا سَڧُواْ دَغَ وَنَّنْ وَنْدَ يَكٜىٰ رِڧٜىٰ دَ تَوْرَرِنَّنْ بَݣَويْ أَ حَنُّنْ دَامَنْسَ، وَنْدَ كُمَ يَكٜىٰ تَڢِيَ ثِكِنْ سَنْدُنَنْ ظِينَارِيَ غُدَا بَݣَويْ مَاسُ رِڧٜىٰ ڢِتِلُ؞
Hausa Bible 1979 (Littafi Mai Tsarki)
“Sai ka rubuta wa mala'ikan ikkilisiyar da take a Afisa haka, ‘Ga maganar wadda take riƙe da taurarin nan bakwai a hannunsa na dama, wadda kuma take tafiya a tsakiyar fitilun nan bakwai na zinariya.