Revelation 20:8 — Compare Translations
3 translations compared side by side
Hausa (Sabon Rai Don Kowa 2020)
zai kuma fito don yă ruɗi al’ummai da suke a kursuyoyi huɗu na duniya, Gog da Magog, yă tattara su don yaƙi. Yawansu kuwa ya yi kamar yashi a bakin teku.
Hausa Arabic 2020 (أَتَّوْرَتْ دَ أَنَّبَاوَا)
ذَيْ كُمَ ڢِتُواْ يَرُوطِ أَلْعُمَّنْ دَسُكٜىٰ أَوَرْوَڟٜىٰ ثِكِنْ دُكَنْ ݣُونَ حُطُ نَدُونِيَا، وَتُواْ، جُوجْ دَ مَاجُوجْ؞ شَيْطَنْ ذَيْ تَتَّرَاسُ دُواْمِنْ يَاڧِ، يَوَنْسُ كُوَ يَيِ كَمَرْ يَشِ عَبَاكِنْ تٜىٰكُ؞
Hausa Bible 1979 (Littafi Mai Tsarki)
ya kuma fito ya yaudari al'ummai waɗanda suke kusurwoyin nan huɗu na duniya, wato, Gog da Magog, ya tattara su saboda yaƙi, yawansu kamar yashin teku.