Revelation 20:9 — Compare Translations
3 translations compared side by side
Hausa (Sabon Rai Don Kowa 2020)
Suka mamaye duk fāɗin duniya suka kuma kewaye sansanin mutanen Allah, birnin da yake ƙauna. Amma wuta ta fito daga sama ta cinye su.
Hausa Arabic 2020 (أَتَّوْرَتْ دَ أَنَّبَاوَا)
سُكَ تَڢِے، سُكَ كُمَ بَظُو كُواْعِنَ أَ ڢَاطِنْ دُونِيَا، سُكَ كٜىٰوَيٜىٰ بِرْنِنْ دَ اللَّهْ يَكٜىٰ ڧَوْنَ، وَتُواْ سَنْسَنِنْ ڟَرْكَكَنْسَ؞ عَمَّا وُتَا تَسَوْكُواْ دَغَ سَمَ تَثِنْيٜىٰسُ؞
Hausa Bible 1979 (Littafi Mai Tsarki)
Sai kuma su bazu, su mamaye duk duniya, su yi wa sansanin tsarkaka da ƙaunataccen birni ƙawanya, sai wuta ta zubo daga sama ta lashe su.