Revelation 21:3 — Compare Translations
3 translations compared side by side
Hausa (Sabon Rai Don Kowa 2020)
Na kuma ji wata babbar murya daga kursiyin tana cewa, “Yanzu mazaunin Allah yana tare da mutane, zai kuma zauna tare da su. Za su zama mutanensa, Allah kansa kuwa zai kasance tare da su yă kuma zama Allahnsu.
Hausa Arabic 2020 (أَتَّوْرَتْ دَ أَنَّبَاوَا)
نَكُمَجِ بَبَّرْ مُرْيَ تَنَ مَغَنَ دَغَ كُجٜىٰرَرْ مُلْكٍ تَنَ ثٜىٰوَ «غَاشِ، وُرِنْ ذَمَنْ اللَّهْ يَنَ تَرٜىٰدَ یَنْ أَدَمْ! ذَيْ ذَوْنَ تَرٜىٰدَسُو، ذَاسُ كُمَ ذَمَ جَمَعَرْسَ؞ اللَّهْ كُوَ دَ كَنْسَ ذَيْ كَسَنْثٜىٰ دَسُو، يَكُمَ ذَمَ اللَّهْ نْسُ؞
Hausa Bible 1979 (Littafi Mai Tsarki)
Na kuma ji wata murya mai ƙara daga kursiyin, tana cewa, “Kun ga, mazaunin Allah na tare da mutane. Zai zauna tare da su, za su zama jama'arsa, Allah kuma shi kansa zai kasance tare da su,