Revelation 3:4 — Compare Translations

3 translations compared side by side

Hausa (Sabon Rai Don Kowa 2020)
Duk da haka kana da mutane kima cikin Sardis waɗanda ba su ɓata tufafinsu ba. Za su yi tafiya tare da ni, saye da fararen tufafi, don sun cancanta.
Hausa Arabic 2020 (أَتَّوْرَتْ دَ أَنَّبَاوَا)
عَمَّا دَيْ حَرْ يَنْذُ أَݣَويْ مُتَنٜىٰ كَطَنْ عَثِكِنْكُ أَ سَرْدِسْ وَطَنْدَ بَسُ ڧَظَنْتَرْدَ رِيغُنَنْسُبَ، ذَاسُيِ تَڢِيَ تَرٜىٰدَنِ سَنْيٜىٰ دَ ڢَرَرٜىٰنْ رِيغُنَ، دُواْمِنْ سُنْ ثَنْثَنْتَ؞
Hausa Bible 1979 (Littafi Mai Tsarki)
Amma dai har yanzu kana da waɗansu kaɗan a Sardisu da ba su ƙazantar da kansu ba, za su kuwa kasance tare da ni da fararen kaya, don sun cancanta.