Revelation 3:9 — Compare Translations
3 translations compared side by side
Hausa (Sabon Rai Don Kowa 2020)
Zan sa waɗanda suke na majami’ar Shaiɗan, waɗanda suke cewa su Yahudawa ne alhali kuwa ba haka ba ne, sai dai maƙaryata, zan sa su zo su fāɗi a ƙasa a gabanka su kuma shaida cewa na ƙaunace ka.
Hausa Arabic 2020 (أَتَّوْرَتْ دَ أَنَّبَاوَا)
غَاشِ، مُتَنٜىٰنَّنْ دَسُكٜىٰ نَڧُنْغِيَرْ شَيْطَنْ، مَاسُ ثٜىٰوَ سُونٜىٰ ذَاٻَٻُّنْ مُتَنٜىٰنْ اللَّهْ عَمَّا كُوَ بَ حَكَ سُكٜىٰ بَ، سُنَ ڧَضْيَا نٜىٰ؞ ذَنْسَا سُذُواْ سُرُسُنَ أَغَبَنْكَ دَ ڢُسْكَرْسُ حَرْ ڧَسَا، سُكُمَ غَانٜىٰ ثٜىٰوَ إِنَ ڧَوْنَرْكَ؞
Hausa Bible 1979 (Littafi Mai Tsarki)
To, ga shi, zan sa su waɗanda suke daga jama'ar Shaiɗan, masu cewa su Yahudawa ne, alhali kuwa ba su ba ne, ƙarya suke yi, zan sa su, su zo, su kwanta a gabanka, su sani dai na ƙaunace ka.