Revelation 4:5 — Compare Translations

3 translations compared side by side

Hausa (Sabon Rai Don Kowa 2020)
Daga kursiyin hasken walƙiya yana ta fitowa, da ƙararraki da kuma tsawa. A gaban kursiyin, fitilu bakwai suna ci. Waɗannan ne ruhohi bakwai na Allah.
Hausa Arabic 2020 (أَتَّوْرَتْ دَ أَنَّبَاوَا)
سَيْ وَلْڧِيَ تَكٜىٰ تَڢِتُواْوَ دَغَ كُجٜىٰرَرْ مُلْكٍ دَ ڧَرَرَّكِ دَ كُمَ ڟَاوَ؞ أَغَبَنْ كُجٜىٰرَرْ مُلْكٍ كُوَ أَݣَويْ ڢِتِلُ بَݣَويْ سُنَ ثِ، وَطَنْدَ سُكٜىٰ رُوحُواْحِنَّنْ بَݣَويْ نَ اللَّهْ ؞
Hausa Bible 1979 (Littafi Mai Tsarki)
Sai walƙiya take ta fitowa daga kursiyin, da ƙararraki, da kuma aradu. A gaban kursiyin kuma fitilu bakwai suna ci, waɗanda suke Ruhohin nan na Allah guda bakwai.