Revelation 5:6 — Compare Translations
3 translations compared side by side
Hausa (Sabon Rai Don Kowa 2020)
Sa’an nan na ga Ɗan Rago, yana kamar an yanka, tsaye a tsakiyar kursiyin, halittu huɗun nan masu rai da kuma dattawan an sun kewaye shi. Yana da ƙahoni bakwai da idanu bakwai, waɗanda suke ruhohi bakwai na Allah da aka aika cikin dukan duniya.
Hausa Arabic 2020 (أَتَّوْرَتْ دَ أَنَّبَاوَا)
سَيْ نَغَ وَنِ طَنْ ضَغُواْ يَنَ ڟَيٜىٰ ڟَكَانِنْ كُجٜىٰرَرْ مُلْكٍ دَ حَلِتُّنَّنْ حُطُ مَاسُ رَيْ؞ دَتَّاوَنَّنْ كُوَ سُنْ كٜىٰوَيٜىٰسُ؞ طَنْ ضَغُوانْ كُوَ يَنَ ڟَيٜىٰ كَمَرْ أَنْيَنْكَشِ؞ يَنَ دَ ڧَهُواْ بَݣَويْ دَ إِدَانُو بَݣَويْ، وَطَنْدَ سُكٜىٰ رُوحُواْحِ بَݣَويْ نَ اللَّهْ وَطَنْدَ عَكَ عَيْكَ أَدُكَنْ دُونِيَا؞
Hausa Bible 1979 (Littafi Mai Tsarki)
Sai na ga wani Ɗan Rago yana a tsaye a tsakiyar kursiyin, kewaye da shi kuma ga rayayyun halittan nan huɗu da dattawan, Ɗan Ragon kuwa kamar yankakke ne, yana da ƙaho bakwai da ido bakwai, waɗanda suke Ruhohin Allah guda bakwai, da aka aika a duniya duka.