Revelation 6:8 — Compare Translations
3 translations compared side by side
Hausa (Sabon Rai Don Kowa 2020)
Na duba, can a gabana kuwa ga ƙodaɗɗen doki! An ba wa mai hawansa suna Mutuwa, Hades kuwa yana biye da shi. Aka ba su iko a kan kashi ɗaya bisa huɗu na duniya don su yi kisa da takobi, yunwa da annoba, har ma da namomin jeji na duniya.
Hausa Arabic 2020 (أَتَّوْرَتْ دَ أَنَّبَاوَا)
دَنَدُوبَ، سَيْغَا وَنِ دُواْكِ وَنْدَ كَلَرْسَ تَكُواْطٜىٰ؞ سُونَنْ مَيْ هَوَنْسَ كُوَ مُتُوَ ثٜىٰ، وُرِنْ ذَمَنْ مَتَتُّو كُمَ يَنَ بِيٜىٰ دَشِ؞ عَكَبَاسُ إِيكُواْ عَكَنْ كَشِ طَيَ بِسَ حُطُ نَمَذَوْنَنْ دُونِيَا، دُواْمِنْ سُكَشٜىٰسُ تَوُرِنْ تَكُواْبِے دَ يُنْوَ دَ بَلَعِ دَ كُمَ نَمُواْمِنْ دَاجِ؞
Hausa Bible 1979 (Littafi Mai Tsarki)
Da na duba, ga doki kili, sunan mahayinsa kuwa Mutuwa, Hades kuma tana biye da shi. Sai aka ba su iko a kan rubu'in duniya, su yi kisa da takobi, da yunwa, da annoba, da kuma namomin jeji na duniya.