Revelation 7:1 — Compare Translations

3 translations compared side by side

Hausa (Sabon Rai Don Kowa 2020)
Bayan wannan, na ga mala’iku huɗu, a tsaye a kusurwoyi huɗu na duniya, suna tsare iskoki huɗu na duniya, domin su hana wani iska hurawa a bisan ƙasa ko a bisan teku ko a bisa wani itace.
Hausa Arabic 2020 (أَتَّوْرَتْ دَ أَنَّبَاوَا)
بَايَنْ وَنَّنْ، سَيْ نَغَ مَلاَىِٕكُ حُطُ سُنَ ڟَيٜىٰ عَكُواْوَثٜىٰ ݣُونَ حُطُ تَدُونِيَا، سُكَ حَنَ إِسْكُواْكِ حُطُنَّنْ نَدُونِيَا هُورَاوَ عَكَنْ ڧَسَا، كُواْ عَكَنْ تٜىٰكُ، كُواْ عَكَنْ وَنِ إِتَاثٜىٰ؞
Hausa Bible 1979 (Littafi Mai Tsarki)
Bayan wannan na ga mala'iku huɗu, a tsaye a kusurwa huɗu ta duniya, suna tsare da iskokin nan huɗu na duniya, don kada wata iska ta busa a kan ƙasa, ko a kan teku, ko a kan wani itace.