Revelation 8:7 — Compare Translations
3 translations compared side by side
Hausa (Sabon Rai Don Kowa 2020)
Mala’ika na fari ya busa ƙahonsa, sai ga ƙanƙara da wuta haɗe da jini, aka kuma wurga su bisan duniya. Kashi ɗaya bisa uku na duniya ya ƙone, kashi ɗaya bisa uku na itatuwa suka ƙone, dukan ɗanyar ciyawa kuma ta ƙone.
Hausa Arabic 2020 (أَتَّوْرَتْ دَ أَنَّبَاوَا)
مَلاَىِٕكَ نَڢَرْكُواْ يَبُوسَ ڧَهُوانْسَ؞ سَيْغَا ڧَنْڧَرَ دَ وُتَا، غَوْرَايٜىٰ دَ جِنِ، عَكَ ظُبَرْ دَسُو عَدُونِيَا؞ وُتَرْ كُمَ تَثِنْيٜىٰ كَشِ طَيَ بِسَ عُكُ نَدُونِيَرْ، تَكُمَ ثِنْيٜىٰ كَشِ طَيَ بِسَ عُكُ نَ عِتَتُوَ دَ دُكَنْ طَنْيٜىٰنْ ثِيَوَ؞
Hausa Bible 1979 (Littafi Mai Tsarki)
Mala'ikan farko ya busa ƙahonsa, sai ga ƙanƙara da wuta, gauraye da jini. Aka zuba su a duniya, sai sulusin duniya ya ƙone, sulusin itatuwa suka ƙone, dukkan ɗanyar ciyawa kuma ta ƙone.