Romans 1:26 — Compare Translations
3 translations compared side by side
Hausa (Sabon Rai Don Kowa 2020)
Saboda wannan, Allah ya yashe su ga sha’awace-sha’awacensu masu banƙyama. Har matansu suka sauya daga haɗuwar mace da miji wadda ita ce daidai bisa ga halitta zuwa haɗuwa da ’yan’uwansu mata wadda ba daidai ba.
Hausa Arabic 2020 (أَتَّوْرَتْ دَ أَنَّبَاوَا)
سَبُواْدَ حَكَ اللَّهْ يَبَاشٜىٰسُ غَ شَعَوَثٜىٰ شَعَوَثٜىٰنْ مَاسُ بَنْ كُنْيَا؞ مَاتَنْسُ كُوَ سُكَ ثَنْجَ دَغَ حَطُوَرْ مَثٜىٰ دَ مِجِ وَدَّ عِتَثٜىٰ دَيْدَيْ بِسَغَ حَلِتَّ ذُوَا إِرِنْ حَطُوَرْ دَ بَ دَيْدَيْبَ؞
Hausa Bible 1979 (Littafi Mai Tsarki)
Don haka Allah ya sallama su ga mugayen sha'awace-sha'awace masu banƙyama, har matansu suka sauya ɗabi'arsu ta halal, da wadda take ta haram.