Romans 10:20 — Compare Translations

3 translations compared side by side

Hausa (Sabon Rai Don Kowa 2020)
Ishaya kuma ya fito gabagadi ya ce, “Waɗanda ba su neme ni ba, su suka same ni; Na bayyana kaina ga waɗanda ba su ma taɓa neman sanina ba.”
Hausa Arabic 2020 (أَتَّوْرَتْ دَ أَنَّبَاوَا)
سَعَنً كُمَ عِشَايَ يَيِ ڧَرْڢِنْ حَلِ حَرْ دَ ثٜىٰوَ اللَّهْ يَثٜىٰ، «وَطَنْدَ بَسُ نٜىٰمٜىٰنِبَ، سُونٜىٰ نَسَا سُكَ سَامٜىٰنِ؞ غَ وَطَنْدَ بَسُ تَمْبَيٜىٰنِبَ، نَبَيَّنَ كَيْنَ؞»
Hausa Bible 1979 (Littafi Mai Tsarki)
Ishayan kuma ya fito gabagaɗi ƙwarai ya ce, “Waɗanda ba su neme ni ba, su suka same ni. Na bayyana kuma ga waɗanda ba su taɓa neman sanina ba.”