Romans 13:4 — Compare Translations

3 translations compared side by side

Hausa (Sabon Rai Don Kowa 2020)
Gama shi bawan Allah ne don kyautata rayuwarka. Amma in ka aikata mugunta, to, sai ka ji tsoro, don ba a banza ne shugaba yake ɗaukan takobinsa ba. Shi fa bawan Allah ne, ta wurinsa ne fushin Allah yakan hukunta masu laifi.
Hausa Arabic 2020 (أَتَّوْرَتْ دَ أَنَّبَاوَا)
غَمَا شِے مَيْ حِدِمَرْ اللَّهْ نٜىٰ سَبُواْدَ أَمْڢَانِنْكَ؞ عَمَّا عِدَنْ كَيْ مَيْيِنْ مُغُنْتَا نٜىٰ، سَيْ كَجِڟُواْرُواْ، دُواْمِنْ بَعَبَنْظَ نٜىٰ شُوغَبَنَّنْ يَكٜىٰ رِڧٜىٰ دَ تَكُواْبِنْ حُكُنْثِبَ؞ شِے مَيْ حِدِمَرْ اللَّهْ نٜىٰ، كُمَ تَوُرِنْسَ ڢُشِنْ اللَّهْ يَكَنْ تَبَّتَا دُواْمِنْ أَ حُكُنْتَ مَيْ مُغُنْتَا؞
Hausa Bible 1979 (Littafi Mai Tsarki)
Domin shi bawan Allah ne, don kyautata zamanka. Amma in kai mai mugun aiki ne, to, ka ji tsoro, don ba a banza yake riƙe da takobi ba. Ai, shi bawa ne na Allah, mai sāka wa mugu da fushi.