Romans 14:10 — Compare Translations

3 translations compared side by side

Hausa (Sabon Rai Don Kowa 2020)
Kai kuwa, don me kake ganin laifin ɗan’uwanka? Ko kuma don me kake rena ɗan’uwanka? Gama duk za mu tsaya a gaban kujerar shari’ar Allah.
Hausa Arabic 2020 (أَتَّوْرَتْ دَ أَنَّبَاوَا)
كَيْ ڢَا، مٜىٰيَسَا كَكٜىٰ غَنِنْ طَنْعُوَنْكَ دَ لَيْڢِے؟ كَيْ كُمَ مٜىٰيَسَا كَكٜىٰ رٜىٰنَ طَنْعُوَنْكَ؟ دُكَنْمُ دَيْ ذَامُ ڟَيَ أَغَبَنْ اللَّهْ وَنْدَ شِينٜىٰ مَيْيِ مَنَ شَرِيعَ؞
Hausa Bible 1979 (Littafi Mai Tsarki)
To, kai, me ya sa kake ganin laifin ɗan'uwanka? Kai kuma, me ya sa kake raina ɗan'uwanka? Ai, dukkanmu za mu tsaya a gaban kursiyin shari'ar Allah.