Romans 14:20 — Compare Translations

3 translations compared side by side

Hausa (Sabon Rai Don Kowa 2020)
Kada ku lalatar da aikin Allah saboda abinci. Dukan abinci mai tsabta ne, sai dai ba daidai ba ne mutum yă ci abin da zai sa wani yă yi tuntuɓe.
Hausa Arabic 2020 (أَتَّوْرَتْ دَ أَنَّبَاوَا)
كَدَ كُرُشٜىٰ عَيْكِنْ اللَّهْ سَبُواْدَ شَعَنِنْ ثِنْ عَبِنْثِ؞ لَلَّيْ كُواْوَنٜىٰ إِرِنْ عَبِنْثِ مَيْ ڟَرْكِے نٜىٰ، عَمَّا مُوغُنْ أَبُ نٜىٰ عِدَنْ عَبِنْثِنْ دَ عَكٜىٰ ثِ يَذَمَ أَبِنْ سَا وَوَنِ تُنْتُٻٜىٰ؞
Hausa Bible 1979 (Littafi Mai Tsarki)
Kada ka rushe aikin Allah saboda abinci kawai. Hakika dukan abu mai tsarki ne, amma mugun abu ne mutum yă zama sanadin tuntuɓe ga wani, ta wurin abin da yake ci.