Romans 14:6 — Compare Translations
3 translations compared side by side
Hausa (Sabon Rai Don Kowa 2020)
Wannan mai ɗaukan rana ɗaya da muhimmanci fiye da sauran, yana yin haka ne ga Ubangiji. Wannan mai cin nama, yana yin haka ne ga Ubangiji, gama yakan yi godiya ga Allah; wannan da ba ya ci kuwa, yana yin haka ne ga Ubangiji yana kuwa yin godiya ga Allah.
Hausa Arabic 2020 (أَتَّوْرَتْ دَ أَنَّبَاوَا)
دُكْ مَيْ غَنِنْ وَتَرَانَ دَ مُهِمَّنْثِ يَنَ يِنْ حَكَنٜىٰ دُواْمِنْ أَغِرْمَمَ عُبَنْغِجِ ؞ دُكْ مَيْ ثِنْ كُواْوَنٜىٰ إِرِنْ عَبِنْثِ يَنَ يِنْ حَكَنٜىٰ دُواْمِنْ أَغِرْمَمَ عُبَنْغِجِ ، غَمَا يَكَنْ بَادَ غُواْدِيَ غَ اللَّهْ سَبُواْدَ عَبِنْثِنْ؞ دُكْ وَنْدَ بَايَ ثِنْ كُواْوَنٜىٰ إِرِنْ عَبِنْثِ شِے مَا يَنَ يِنْ حَكَنٜىٰ دُواْمِنْ أَغِرْمَمَ عُبَنْغِجِ ، غَمَا شِيمَا يَكَنْيِ وَ اللَّهْ غُواْدِيَ؞
Hausa Bible 1979 (Littafi Mai Tsarki)
Mai kiyaye wata rana musamman, yana kiyaye ta ne saboda Ubangiji. Mai cin nan kuma, yana ci ne saboda Ubangiji, da yake yana gode wa Allah. Marar cin nan kuma yana ƙin ci ne saboda Ubangiji, shi ma kuwa yana gode wa Allah.