Romans 16:19 — Compare Translations

3 translations compared side by side

Hausa (Sabon Rai Don Kowa 2020)
Kowa ya riga ya ji game da biyayyarku, don haka ina cike da farin ciki game da ku; amma ina so ku zama masu hikima game da abin da yake nagari, ku kuma zama marasa laifi ga abin da yake mugu.
Hausa Arabic 2020 (أَتَّوْرَتْ دَ أَنَّبَاوَا)
كُواْوَ يَجِ لَابَرِ يَدَّ كُكٜىٰيِنْ بِيَيَّ، وَنَّنْ كُوَ يَسَا إِنَ ڢَضٍ ثِكِ سَبُواْدَكُو؞ عَمَّا إِنَ سُواْ كُذَمَ مَاسُ حِكِمَ غَ أَبِنْدَ يَكٜىٰ مَيْݣَوْ، كُكُمَ ذَمَ مَرَسَ لَيْڢِے غَ دُكْ أَبِنْدَ يَشَاڢِ مُغُنْتَا؞
Hausa Bible 1979 (Littafi Mai Tsarki)
Amma ku kam, ai, kowa ya san biyayyarku, shi ya sa nake farin ciki da ku. Sai dai ina so ku gwanance da abin da yake nagari, amma ya zama ba ruwanku da mugunta.