Romans 2:12 — Compare Translations
3 translations compared side by side
Hausa (Sabon Rai Don Kowa 2020)
Duk waɗanda suka yi zunubi a rashi sanin doka, a rashin doka za su hallaka, waɗanda kuma suka yi zunubi ƙarƙashin doka, a ƙarƙashin doka za a hukunta su.
Hausa Arabic 2020 (أَتَّوْرَتْ دَ أَنَّبَاوَا)
دُكْ مَاسُ يِنْ ذُنُوبِ بَاتَرٜىٰدَ سَنِنْ كُواْيَرْوَرْ مُوسَٰى بَ، ذَاسُ هَلَّكَ بَاتَرٜىٰدَ كُواْيَرْوَرْ بَ، عَمَّا دُكْ مَاسُ يِنْ ذُنُوبِ ثِكِنْ سَنِنْ كُواْيَرْوَرْ، ذَاعَ حُكُنْتَسُ بِسَغَ كُواْيَرْوَرْ؞
Hausa Bible 1979 (Littafi Mai Tsarki)
Ɗaukacin waɗanda suka yi zunubi a rashin sanin Shari'a, za su hallaka ne ba tare da Shari'a ba. Ɗaukacin waɗanda suka yi zunubi a ƙarƙashin Shari'a kuwa, za a hukunta su ta hanyar Shari'a.