Romans 2:15 — Compare Translations
3 translations compared side by side
Hausa (Sabon Rai Don Kowa 2020)
To, da yake sun nuna cewa abubuwan da dokar take bukata suna a rubuce a zukatansu, lamirinsu yana kuma ba da shaida, tunaninsu kuwa yanzu yana zarginsu ko kuma yana kāre su.
Hausa Arabic 2020 (أَتَّوْرَتْ دَ أَنَّبَاوَا)
أَيُّكَنْسُ سُنْ نُونَ ثٜىٰوَ أَبِنْدَ كُواْيَرْوَرْ تَثٜىٰ عَيِ يأَنَانً أَرُبُوثٜىٰ ثِكِنْ ظُكَاتَنْسُ؞ عَثِكِنْ تُنَانِنْ ظُكَاتَنْسُ كُوَ أَݣَويْ شَيْدَ غَمٜىٰدَ وَنَّنْ، غَمَا تُنَانِنْسُ يَكَنْ سَامٜىٰسُ دَ لَيْڢِے أَوَنِ لُواْكَثِ، أَوَنِ لُواْكَثِ كُمَ بَايَ سَامُنْسُ دَ لَيْڢِے؞
Hausa Bible 1979 (Littafi Mai Tsarki)
Ayyukansu sun nuna, cewa abin da Shari'a ta umarta a rubuce yake a cikin zukatansu, lamirinsu kuwa yana shaidawa, tunaninsu kuwa yana zarginsu, ko kuma yana kāre su.