Romans 5:14 — Compare Translations
3 translations compared side by side
Hausa (Sabon Rai Don Kowa 2020)
Duk da haka, mutuwa ta yi mulki tun Adamu har yă zuwa Musa, ta yi mulki har ma a kan waɗanda ba su yi zunubi ta wurin taka umarni kamar yadda Adamu ya yi ba. A wata hanya dai Adamu shi ne kwatancin wani mutumin nan mai zuwa.
Hausa Arabic 2020 (أَتَّوْرَتْ دَ أَنَّبَاوَا)
دُكْدَهَكَ مُتُوَ تَايِ مُلْكِ عَكَنْ مُتَنٜىٰ دُكَ دَغَ زَامَانِنْ ءَادَمُ ذُوَا زَامَانِنْ مُوسَٰى، حَرْ مَا تَيِ إِيكُواْ عَكَنْ وَطَنْدَ ذُنُبَنْسُ بَ نَكَرْيَ دُواْكَا بَنٜىٰ كَمَرْ يَدَّ نَ ءَادَمُ يَكَسَنْثٜىٰ؞ ءَادَمُ كُوَ ݣُوتَنْثِنْ وَنْدَ يَكٜىٰ ݣَوْتَرْ اللَّهْ مَيْ ذُوَانَّنْ؞
Hausa Bible 1979 (Littafi Mai Tsarki)
Duk da haka kuwa mutuwa ta mallaka tun daga Adamu har ya zuwa Musa, har ma a kan waɗanda ba su yi zunubi irin na keta umarnin da adamu ya yi ba, wanda yake shi ne kwatancin mai zuwan nan.