Romans 7:3 — Compare Translations
3 translations compared side by side
Hausa (Sabon Rai Don Kowa 2020)
Saboda haka fa, in ta auri wani yayinda mijinta yana raye, za a ce da ita mazinaciya. Amma in mijinta ya mutu, an sake ta ke nan daga wannan doka, ita kuwa ba mazinaciya ba ce, ko da yake ta auri wani.
Hausa Arabic 2020 (أَتَّوْرَتْ دَ أَنَّبَاوَا)
سَبُواْدَ حَكَ عِدَنْ تَا عَوْرِ وَنِ دَبَمْ سَعَدَّ مِجِنْتَ يَنَدَ رَيْ، ذَاعَ ثٜىٰ دَ عِتَ مَيْ ظِنَ؞ عَمَّا عِدَنْ مِجِنْتَ يَمُتُ تَنَدَ یَنْثِ كٜىٰنَنْ بِسَغَ كُواْيَرْوَرْ طَوْرِنْ عَوْرٜىٰ؞ عِدَنْ كُوَ تَسَاكٜىٰ عَوْرِ وَنِ، عِتَ بَمَيْ ظِنَ بَثٜىٰ؞
Hausa Bible 1979 (Littafi Mai Tsarki)
Don haka, muddin mijinta yana da rai, in ta auri wani, sai a kira ta mazinaciya. Amma in mijinta ya mutu, ta kuɓuta daga igiyar wannan aure, ko da ta auri wani kuwa, ita ba mazinaciya ba ce.