Romans 9:17 — Compare Translations
3 translations compared side by side
Hausa (Sabon Rai Don Kowa 2020)
Gama Nassi ya ce wa Fir’auna, “Na ɗaga ka saboda wannan manufa, saboda in nuna ikona a cikinka domin kuma a shaida sunana a duniya duka.”
Hausa Arabic 2020 (أَتَّوْرَتْ دَ أَنَّبَاوَا)
غَمَا رُبُوتَثِّيَرْ مَغَنَرْ اللَّهْ تَثٜىٰ وَ ڢِرْعَوْنَ «نَتَاشٜىٰكَ كَذَمَ سَرْكِے دَنُڢِ ثٜىٰوَ إِنْ نُونَ إِيكُواْنَ تَوُرِنْكَ، عَكُمَ سَنَرْدَ سُونَنَ ثِكِنْ دُونِيَا دُكَ؞»
Hausa Bible 1979 (Littafi Mai Tsarki)
Don a Nassi an ce da Fir'auna, “Na girmama ka ne musamman, domin in nuna ikona a kanka, domin kuma a sanar da sunana a duniya duka.”