Ruth 2:11 — Compare Translations
3 translations compared side by side
Hausa (Sabon Rai Don Kowa 2020)
Bowaz ya amsa, “An faɗa mini duka game da abin kika yi domin surukarki tun mutuwar mijinki, yadda kika bar mahaifinki da mahaifiyarki da kuma ƙasarki kika zo ki yi zama da mutanen da ba ki taɓa sani ba.
Hausa Arabic 2020 (أَتَّوْرَتْ دَ أَنَّبَاوَا)
سَيْ بُواْوَظْ يَأَمْسَ يَثٜىٰ «أَنْ ڢَطَا مِنِ إِرِنْ ڧَوْنَ دَ كِرْكِنْ دَ كِكَيِ وَمَامَرْ مِجِنْكِ تُنْ مُتُوَرْ مِجِنْكِ؞ إِنَ سَنٜىٰ دَ يَدَّ كِكَ بَرْ إِيَايٜىٰنْكِ دَ ڧَسَرْكِے دَ يَدَّ كِكَ ذُواْ وُرِنْ مُتَنٜىٰنْ دَ بَاكِ تَٻَ سَنِنْسُبَ أَدَا؞
Hausa Bible 1979 (Littafi Mai Tsarki)
Amma Bo'aza ya ce mata, “An faɗa mini dukan abin da kika yi wa surukarki tun lokacin da mijinki ya rasu, da yadda kika bar iyayenki da ƙasarku, kika zo wurin mutanen da ba ki taɓa saninsu ba a dā.