Ruth 2:13 — Compare Translations

3 translations compared side by side

Hausa (Sabon Rai Don Kowa 2020)
Ta ce, “Bari in ci gaba da samun tagomashi a idanunka ranka yă daɗe. Ka ta’azantar da ni ka kuma yi wa baranyarka magana mai alheri ko da yake ban kai matsayi ɗaya daga cikin bayinka ’yan mata ba.”
Hausa Arabic 2020 (أَتَّوْرَتْ دَ أَنَّبَاوَا)
سَيْ رُوتْ تَثٜىٰ «مَيْغِرْمَ، بَرِ إِنْيِ تَسَامُنْ ڢَضٍ جِنِ أَغَبَنْكَ؞ كَيِ وَبَيْوَرْكَ مَغَنَ مَيْ ڧَرْڢَڢَاوَرْ ذُوثِيَا، كُواْدَيَكٜىٰ بَنْ كَيْ طَيَ دَغَ ثِكِنْ بَايِنْكَ دَرَجَبَ؞»
Hausa Bible 1979 (Littafi Mai Tsarki)
Rut ta ce, “Shugaba, kā yi mini alheri ƙwarai, gama kā ta'azantar da ni, kā yi wa baiwarka maganar alheri, ko da yake ni ba ɗaya daga cikin barorinka ba ce.”