Ruth 3:10 — Compare Translations
3 translations compared side by side
Hausa (Sabon Rai Don Kowa 2020)
Sai ya amsa ya ce, “ Ubangiji yă albarkace ki ’yata. Wannan alheri ya fi wannan da kika nuna da farko. Ba ki gudu kin bi saurayi, mai arziki ko matalauci ba.
Hausa Arabic 2020 (أَتَّوْرَتْ دَ أَنَّبَاوَا)
سَيْ بُواْوَظْ يَثٜىٰ « يَهْوٜىٰهْ يَ أَلْبَرْكَثٜىٰكِ، یَتَ؞ دُواْمِنْ وَنَّنْ أَمِنْثِنْ دَ كِكَ نُونَ وَ دَنْغِنْمُ يَنْذُ يَڢِ وَنْدَ كِكَ رِغَا كِنْ نُونَاوَ مَامَرْ مِجِنْكِ؞ غَمَا بَكِنٜىٰمِ سَوْرَيِبَ، كُواْ شِے مَيْ أَرْزِڧِ نٜىٰ كُواْ تَلَكَ نٜىٰ؞
Hausa Bible 1979 (Littafi Mai Tsarki)
Sa'an nan ya ce, “Ubangiji ya sa miki albarka 'yata, yanzu kin nuna alheri mafi girma fiye da na dā da yake ba ki nemi saurayi, matalauci ko attajiri ba.