Ruth 4:1 — Compare Translations
3 translations compared side by side
Hausa (Sabon Rai Don Kowa 2020)
Ana cikin haka Bowaz ya haura zuwa ƙofar gari ya tafi ya zauna a can. Sa’ad da dangi mai fansan da ya yi zance ya iso, Bowaz ya ce, “Zo nan abokina ka zauna.” Saboda haka ya ratso ya zauna.
Hausa Arabic 2020 (أَتَّوْرَتْ دَ أَنَّبَاوَا)
أَنَانً سَيْ بُواْوَظْ يَتَڢِے وُرِنْ تَارُوَ ثِكِنْ ڧُواْڢَرْ غَرِ يَذَوْنَ؞ سَيْكُوَ غَا مُتُمِنْ دَنْغِ نَكُسَ، وَنَّنْ دَ بُواْوَظْ يَيِظَنْثٜىٰ عَكَيْ، يَنَ وُثٜىٰوَ؞ سَيْ بُواْوَظْ يَكِرَشِ يَثٜىٰ «أَبُواْكِ، كَذُواْ نَنْ كَذَوْنَ؞» سَيْ يَجٜىٰ يَذَوْنَ؞
Hausa Bible 1979 (Littafi Mai Tsarki)
Bo'aza fa ya tafi, ya zauna a dandalin ƙofar gari. Sai ga wani daga cikin waɗanda hakkinsu ne su ɗauki Rut, shi ne kuwa wanda Bo'aza ya ambata, ya iso. Bo'aza kuwa ya ce masa, “Ratso nan, wāne, ka zauna.” Sai ya ratsa, ya zauna.