Ruth 4:10 — Compare Translations
3 translations compared side by side
Hausa (Sabon Rai Don Kowa 2020)
Na kuma ɗauki Rut mutuniyar Mowab, gwauruwar Malon a matsayin matata domin sunan mamaci da kuma mallakarsa yă ci gaba, domin kada sunansa yă ɓace daga cikin iyali ko daga tarihin gari. A yau ku ne shaidu!”
Hausa Arabic 2020 (أَتَّوْرَتْ دَ أَنَّبَاوَا)
ذَنْ كُمَ طَوْكِ رُوتْ یَرْ ڧَسَرْ مُواْوَبْ مَاتَرْ مَلُوانْ وَنْدَ يَمُتُ؞ تَهَكَ ذَاعَ عِيَ حَيْڢِ يَرُواْ وَنْدَ ذَيْغَاجِ أَبِنْدَ مِجِنْتَ يَكٜىٰدَشِ، يَكُمَ أَمْسَ سُونَنْسَ، دُواْمِنْ كَدَ سُونَنْسَ يَمُتُ ثِكِنْ دَنْغِنْسَ دَ كُمَ غَرِنْسَ؞ يَوْ كُو شَيْدُ نٜىٰ؞»
Hausa Bible 1979 (Littafi Mai Tsarki)
Game da wannan kuma Rut, mutuniyar Mowab, matar marigayi Malon, ta zama matata domin in wanzar da sunan marigayin cikin gādonsa, don kada sunansa ya mutu daga na 'yan'uwansa, da kuma a garinsu. Ku ne fa shaidu a yau.”