Ruth 4:5 — Compare Translations

3 translations compared side by side

Hausa (Sabon Rai Don Kowa 2020)
Sa’an nan Bowaz ya ce, “A ranar da ka saya filin daga Na’omi da kuma daga Rut mutuniyar Mowab, ka sayi gwauruwar marigayin nan, domin ka riƙe sunan marigayin da kuma kayansa.”
Hausa Arabic 2020 (أَتَّوْرَتْ دَ أَنَّبَاوَا)
سَعَنً بُواْوَظْ يَثٜىٰ مَسَ «تُواْ، رَانَرْدَ كَسَيِ غُواْنَرْ دَغَ حَنُّنْ نَعُواْمِ، ذَاكَ كُمَ طَوْكِ رُوتْ یَرْ ڧَسَرْ مُواْوَبْ، وَدَّ مِجِنْتَ يَمُتُ؞ تَهَكَ ذَاعَ سَامِ یَیَنْ دَ ذَاسُ أَمْسَ سُونَنْ مِجِنْتَ دَ يَمُتُ، سُكُمَ مَلَّكِ رَبُوانْ غَادُوانْسَ؞»
Hausa Bible 1979 (Littafi Mai Tsarki)
Sa'an nan Bo'aza ya ce, “A ranar da ka sayi gonar daga hannun Na'omi, sai kuma ka ɗauki Rut, mutuniyar Mowab, matar marigayin, domin ka ta da zuriyar da za ta gaji marigayin.”