Ruth 4:7 — Compare Translations
3 translations compared side by side
Hausa (Sabon Rai Don Kowa 2020)
(To, a kwanakin can a Isra’ila, domin a tabbatar da fansa da kuma musayar da mallaka, mutum zai cire takalminsa ya ba wa ɗayan. Wannan ita ce hanyar tabbatar da al’amarin a hukumance a cikin Isra’ila.)
Hausa Arabic 2020 (أَتَّوْرَتْ دَ أَنَّبَاوَا)
أَ زَامَانِنْ دَا عَ إِسْرَٰٓءِيلَاوَا أَݣَويْ وَتَ أَلْعَادَا ثٜىٰوَ دُكْ وَنْدَ يَكٜىٰبَا وَنِ دَامَرْ ڢَنْسَ كُواْ سَيٜىٰنْ أَبُ، يَكَنْ ثِرٜىٰ تَاكَلْمِنْسَ يَبَا مَيْ كَرْٻَرْ دَامَرْ ڢَنْسَرْ كُواْ سَيٜىٰنْ؞ يِنْ حَكَنٜىٰ يَكَنْ تَبَّتَرْ دَ ذَنْثٜىٰنْ أَعِدُوانْ جَمَعَ؞
Hausa Bible 1979 (Littafi Mai Tsarki)
Wannan ita ce al'adar Isra'ilawa a dā a kan sha'anin fansa ko musaya, don tabbatar da al'amarin. Sai mai sayarwar ya tuɓe takalminsa ya ba mai sayen. Wannan ita ce hanyar tabbatarwa a cikin Isra'ila.