Song of Solomon 4:11 — Compare Translations

3 translations compared side by side

Hausa (Sabon Rai Don Kowa 2020)
Leɓunanki suna zub da zaƙi kamar kakin zuma, amaryata; madara da zuma suna a ƙarƙashin harshenki. Ƙanshin rigunanki ya yi kamar na Lebanon.
Hausa Arabic 2020 (أَتَّوْرَتْ دَ أَنَّبَاوَا)
يَا كٜىٰ أَمَرْيَتَ، ذَاڧِنْ لٜىٰٻُنَنْكِ كَمَرْ ظُمَ يَكٜىٰ، مَدَرَ دَ ظُمَ سُنَ ڧَرْڧَشِنْ هَرْشٜىٰنْكِ؞ ڧَنْشِنْ تُڢَاڢِنْكِ يأَنَانً كَمَرْ نَڧَنْشِنْ تُرَارٜىٰنْ لٜىٰبَنُوانْ؞
Hausa Bible 1979 (Littafi Mai Tsarki)
Zaƙin leɓunanki kamar zuma ne, ya budurwata, A gare ni harshenki madara ne da zuma. Tufafinki suna ƙanshi kamar turaren da yake cikin Dutsen Lebanon.