Song of Solomon 5:15 — Compare Translations

3 translations compared side by side

Hausa (Sabon Rai Don Kowa 2020)
Ƙafafunsa sun yi kamar ginshiƙan dutsen alabastar da aka kafa su a cikin rammukar zinariya. Kamanninsa ya yi kamar Lebanon, mafi kyau kamar itacen al’ul nasa.
Hausa Arabic 2020 (أَتَّوْرَتْ دَ أَنَّبَاوَا)
ثِنْيُواْيِنْسَ كَمَرْ غِنْشِڧَنْ دَ عَكَيِ دَ دُوڟٜىٰنْ عُواْنِسْ، عَكَ كَڢَسُ عَكَنْ تُوشٜىٰنْ ظِينَارِيَ؞ كَمَنِّنْسَ كَمَرْ دَرَجَرْ لٜىٰبَنُوانْ نٜىٰ، كَمَرْ عِتَتُوَنْ سٜىٰدَ مَڢِے ݣَوْ؞
Hausa Bible 1979 (Littafi Mai Tsarki)
Cinyoyinsa kamar ginshiƙan da aka yi da dutsen alabasta, Aka kafa su a cikin kwasfar zinariya. Kamanninsa kamar Dutsen Lebanon ne, Da itatuwan al'ul ɗinsa mafi kyau.