Song of Solomon 7:13 — Compare Translations
3 translations compared side by side
Hausa (Sabon Rai Don Kowa 2020)
Manta-uwa sun ba da ƙanshinsu, a bakin ƙofa kuwa akwai kowane abinci mai daɗi, sabo da tsoho, da na ajiye dominka, ƙaunataccena.
Hausa Arabic 2020 (أَتَّوْرَتْ دَ أَنَّبَاوَا)
سَيْوَرْ طَوْكَرْ ثِكِ تَنَ بَظَ ڧَنْشِنْتَ أَوُرِنْ؞ یَیَنْ عِتَتُوَ مَاسُ دَاطِے، سَابَبِّے دَ وَطَنْدَ نَأَجِيٜىٰ تُنْدَا، سُنَانَنْ كُسَ عَبَاكِنْ ڧُواْڢَرْمُ، نَأَجِيٜىٰسُ دُواْمِنْكَ، يَا ڧَوْنَتَثّٜىٰنَ؞
Hausa Bible 1979 (Littafi Mai Tsarki)
Za ka ji ƙanshin shuke-shuke Da na dukan 'ya'yan itatuwa masu daɗi. Na adana maka jin daɗi na dā da na yanzu, ya ƙaunataccena.