Titus 1:7 — Compare Translations
3 translations compared side by side
Hausa (Sabon Rai Don Kowa 2020)
Da yake an danƙa wa mai kula da ikkilisiya riƙon amana saboda Allah, dole yă zama marar aibi ba mai girman kai ba, ba mai saurin fushi ba, ba mai buguwa ba, ba mai rikici ba, ba kuma mai son ƙazamar riba ba.
Hausa Arabic 2020 (أَتَّوْرَتْ دَ أَنَّبَاوَا)
تُنْدَيَكٜىٰ مَيْ كُلَ دَ جَمَعَرْ مَاسُبِے مَيْ رِڧُوانْ أَمَانَرْ اللَّهْ نٜىٰ، دُواْلٜىٰنٜىٰ يَكَسَنْثٜىٰ مَرَرْ لَيْڢِے غَ كُواْوَ؞ كَدَ يَذَمَ مَيْ نُونَ إِيكُواْ، كُواْ مَيْ سَوْرِنْ ڢُشِے، كُواْ مَيْ بُغُوَ، كُواْ مَيْ سَوْرِنْ دُوكَ، كُواْ كُوَ مَيْ ݣُوطَيِنْ ڧَظَامَرْ رِيبَ؞
Hausa Bible 1979 (Littafi Mai Tsarki)
Lalle ne kuwa, kowane mai kula da ikkilisiya, da yake shi mai riƙon amana saboda Allah ne, yă zama marar abin zargi, ba mai taurinkai ba, ko mai saurin fushi, ko mashayi, ko mai saurin dūka, ko mai kwaɗayin ƙazamar riba.