Titus 3:14 — Compare Translations
3 translations compared side by side
Hausa (Sabon Rai Don Kowa 2020)
Dole mutanenmu su koyi ba da kansu ga aikata abin da yake nagari, domin su iya biyan bukatunsu na yau da kullum kada kuma su yi rayuwar marar amfani.
Hausa Arabic 2020 (أَتَّوْرَتْ دَ أَنَّبَاوَا)
دُواْلٜىٰ مُتَنٜىٰنْمُ سُ كُواْيِ يَدَّ ذَاسُ مِيڧَ كَنْسُ غَ عَيْكَتَ أَيُّكَ مَاسُ ݣَوْ، دُواْمِنْ سُإِيَ بَادَ تَيْمَكُواْ وَجٜىٰنْ بِيَنْ مُهِمَّنْ بُڧَاتُو؞ كَدَ سُيِ رَايُوَا مَرَرْ أَمْڢَانِ؞
Hausa Bible 1979 (Littafi Mai Tsarki)
Jama'armu su koyi himmantuwa ga aikin kirki don biyan bukatun matsattsu, kada su zama marasa amfani.