Zechariah 1:19 — Compare Translations
3 translations compared side by side
Hausa (Sabon Rai Don Kowa 2020)
Na tambayi mala’ikan da yake mini magana, na ce, “Mene ne waɗannan?” Ya amsa mini ya ce, “Waɗannan su ne ƙahonin da suka watsar da Yahuda, Isra’ila da kuma Urushalima.”
Hausa Arabic 2020 (أَتَّوْرَتْ دَ أَنَّبَاوَا)
سَيْ نَثٜىٰ وَمَلاَىِٕكَنْ دَ يَيِ مَغَنَ دَنِے «مٜىٰنٜىٰنٜىٰ مَعَنَرْ وَطَنَّنْ؟» سَيْيَأَمْسَ يَثٜىٰ «وَطَنَّنْ ڧَهُواْنِ سُونٜىٰ عَلَمَرْ إِيكُواْكِنْ أَلْعُمَّنْ دَ سُكَ وَرْوَاڟَرْدَ يَهُودَ دَ إِسْرَٰٓءِيلَ دَ عُرُوشَلِيمَ؞»
Hausa Bible 1979 (Littafi Mai Tsarki)
Sai na ce wa mala'ikan da ya yi magana da ni, “Mene ne waɗannan?” Shi kuwa ya ce mini, “Waɗannan su ne ƙahonin da suka warwatsa Yahuza, da Isra'ila, da Urushalima.”