Zechariah 1:21 — Compare Translations

3 translations compared side by side

Hausa (Sabon Rai Don Kowa 2020)
Na yi tambaya na ce, “Mene ne waɗannan suke zuwa yi?” Ya amsa ya ce, “Waɗannan ne ƙahonin da suka watsar da Yahuda har ba wanda yake iya ɗaga kansa, amma maƙeran sun zo don su tsorata su su kuma saukar da ƙahonin ƙasashen nan waɗanda suka ɗaga ƙahoninsu gāba da ƙasar Yahuda don su warwatsa ta.”
Hausa Arabic 2020 (أَتَّوْرَتْ دَ أَنَّبَاوَا)
سَيْ نَثٜىٰ «مٜىٰنٜىٰنٜىٰ مُتَنٜىٰ حُطُنَّنْ سُكٜىٰ ذُوَايِ؟» سَيْ يَهْوٜىٰهْ يَثٜىٰ «وَطَنَّنْ ڧَهُواْنِ سُونٜىٰ أَلْعُمَّنْ دَ سُكَ وَرْوَاڟَرْدَ يَهُودَ حَرْ مُتُمْ بَايَ عِيَ طَغَ كَنْسَ؞ عَمَّا وَطَنَّنْ مَڧٜىٰرَ حُطُ سُنْ ذُواْ دُواْمِنْ سُڟُواْرَتَرْ دَ أَلْعُمَّنْ، سُكَرْيَ ڧَهُواْنِنْ أَلْعُمَّنْ دُونِيَا وَطَنْدَ سُكَ طَغَ ڧَهُواْنِنْسُ سُنَ غَابَادَ ڧَسَرْ يَهُودَ؞»
Hausa Bible 1979 (Littafi Mai Tsarki)
Sai na ce, “Me waɗannan suke zuwa su yi?” Sai ya ce, “Waɗannan su ne ƙahonin da suka warwatsa Yahuza don kada mutum ya ɗaga kansa. Waɗannan kuwa sun zo don su tsorata su, su karya ƙahonin al'umman duniya waɗanda suka ɗaga ƙahoninsu gāba da ƙasar Yahuza don su warwatsa ta.”