Zechariah 10:1 โ Compare Translations
3 translations compared side by side
Hausa (Sabon Rai Don Kowa 2020)
Ku roฦi Ubangiji yฤ ba ku ruwa a lokacin bazara; Ubangiji ne yake yin gizagizan hadari. Shi ne yake ba wa mutane yayyafin ruwan sama yana kuma ba da tsire-tsire na fili ga kowa.
Hausa Arabic 2020 (ุงููุชููููุฑูุชู ุฏู ุงูููููุจูุงููุง)
ููุถููุงฺูงู ุถููู ุณูู
ู ุฏูุบู ููููููููฐูู ุงูู ูููุงูููุซููู ุฏูุงู
ูููุ ุฏูุบู ููููููููฐูู ููููุฏู ููููููฐูููู ุบูุฑูุบูุฌูููฐูู ุถูููุ ููููุฏู ููููููฐ ุจูุงุฏู ุถููู ุณูู
ู ุบู ู
ูุชูููููฐุ ุฏู ููู
ู ฺูุฑูููฐ ฺูุฑูููฐ ุบู ูููุงูููููููฐ ู
ูุชูู
ูุ
Hausa Bible 1979 (Littafi Mai Tsarki)
Ku roฦi ruwan sama daga wurin Ubangiji a lokacin bazara, Gama Ubangiji ne yake yin gizagizan hadiri, Shi ne yake bai wa mutane yayyafi. Shi ne kuma yake ba kowane mutum tsire-tsiren saura.