Zechariah 10:3 — Compare Translations
3 translations compared side by side
Hausa (Sabon Rai Don Kowa 2020)
“Ina fushi da makiyayan, zan kuma hukunta shugabannin; gama Ubangiji Maɗaukaki zai lura da garkensa, wato, gidan Yahuda, zai kuma sa su zama kamar doki mai fariya cikin yaƙi.
Hausa Arabic 2020 (أَتَّوْرَتْ دَ أَنَّبَاوَا)
ڢُشِنَ يَنَ ڧُونَ عَكَنْ مَكِيَايَنْ، ذَنْ كُوَ حُكُنْتَ شُوغَبَنِّنْ؞ أَيْ، نِے يَهْوٜىٰهْ مَيْ ضُنْدُنَا نَظِيَرْثِ جَمَعَتَ، نَظِيَرْثِ غِدَنْ يَهُودَ؞ ذَنْ مَيْدَ غَرْكٜىٰنْ تُمَكِينَ دَوَكِنْ يَاڧِنَ مَاسُ ڧَرْڢِے؞
Hausa Bible 1979 (Littafi Mai Tsarki)
Ubangiji ya ce, “Ina fushi ƙwarai da makiyayan, Zan kuwa hukunta shugabannin, Gama ni Ubangiji Mai Runduna zan lura da garkena, Wato jama'ar Yahuza. Zan mai da su dawakaina na yaƙi.