Zechariah 12:4 — Compare Translations

3 translations compared side by side

Hausa (Sabon Rai Don Kowa 2020)
A ranan nan zan sa kowane doki yă tsorata, mai hawan dokin kuma yă haukace,” in ji Ubangiji. “Zan sa idanuna in tsare gidan Yahuda, amma zan makantar da dukan dawakan al’ummai.
Hausa Arabic 2020 (أَتَّوْرَتْ دَ أَنَّبَاوَا)
إِنْجِ يَهْوٜىٰهْ «أَ رَانَرْ نَنْ ذَنْسَا كُواْوَنٜىٰ دُواْكِنْ أَبُواْكَنْ غَابَا يَضِكِثِے، مَيْ هَوَنْسَ كُمَ يَهَوْكَثٜىٰ؞ عَمَّا ذَنْ كَڢَ عِدَنُونَ عَكَنْ غِدَنْ يَهُودَ، سَعَدَّ نَسَا كُواْوَنٜىٰ دُواْكِ نَڧَبِيلُنْ يَذَمَ مَكَهُواْ؞
Hausa Bible 1979 (Littafi Mai Tsarki)
A wannan rana zan firgita kowane doki, in sa mahayinsa ya haukace. Zan lura da mutanen Yahuza, amma zan makantar da dawakan abokan gābansu.