Zechariah 14:10 — Compare Translations
3 translations compared side by side
Hausa (Sabon Rai Don Kowa 2020)
Ƙasar gaba ɗaya daga Geba zuwa Rimmon, kudu da Urushalima, za tă zama kamar Araba. Amma Urushalima za tă kasance a wurinta, daga Ƙofar Benyamin zuwa sashen Ƙofa ta Farko, zuwa Ƙofar Kusurwa, daga kuma Hasumiyar Hananel zuwa wurin matsin ruwan inabin sarki.
Hausa Arabic 2020 (أَتَّوْرَتْ دَ أَنَّبَاوَا)
ڧَسَا دُكَ ذَاتَ ذَمَ ڢِيلِ دَغَ غٜىٰبَ ذُوَا رِمُّوانْ عَكُدَنْثِنْ عُرُوشَلِيمَ؞ عَمَّا عُرُوشَلِيمَ ذَاتَ ثِيغَبَدَ كَسَنْثٜىٰوَ عَكَنْ تُدُ عِنْدَ تَكٜىٰ ذَمَنْتَ؞ دَغَ ڧُواْڢَرْ بِلِيَامِنُ ذَاتَ مِيڧٜىٰ ذُوَا ڧُواْڢَرْ ݣُونَ عِنْدَ دَا أَݣَويْ ڧُواْڢَ؞ ذَاتَ كُمَ مِيڧٜىٰ دَغَ حَصُومِيَا تَ هَنَنٜىٰلْ ذُوَا وُرَارٜىٰنْ مَڟٜىٰوَرْ ضُوً إِنَبِے وَطَنْدَ سُكٜىٰ نَسَرْكِے؞
Hausa Bible 1979 (Littafi Mai Tsarki)
Ƙasa dukka za ta zama fili, daga Geba zuwa Rimmon a kudancin Urushalima. Amma Urushalima za ta kasance a kan tudu, za ta miƙe daga Ƙofar Biliyaminu, zuwa wurin da ƙofa ta fari take a dā, har zuwa Ƙofar Kusurwa, sa'an nan ta miƙe daga Hasumiyar Hananel zuwa wuraren matsewar ruwan inabin sarki.