Zechariah 14:20 — Compare Translations
3 translations compared side by side
Hausa (Sabon Rai Don Kowa 2020)
A ranan nan za a rubuta TSARKI GA Ubangiji a jikin ƙararrawar dawakai, kuma tukwanen dahuwa a gidan Ubangiji za su zama kamar kwanoni masu tsarki a gaban bagade.
Hausa Arabic 2020 (أَتَّوْرَتْ دَ أَنَّبَاوَا)
أَ رَانَرْ نَنْ ذَاعَ رُبُوتَ وَطَنَّنْ كَلْمُواْمِ حَرْ عَكَنْ ڧَرَرَّوَرْ دَوَكِنْ، «أَنْ كٜىٰٻٜىٰ دَ ڟَرْكِے غَ يَهْوٜىٰهْ»؞ تُݣُونٜىٰنْ دَسُكٜىٰ أَ غِدَنْ يَهْوٜىٰهْ ذَاعَ كٜىٰٻٜىٰسُ كَمَرْ ݣُونُواْنِنْ دَسُكٜىٰ أَغَبَنْ بَغَدٜىٰ؞
Hausa Bible 1979 (Littafi Mai Tsarki)
A wannan rana za a zāna waɗannan kalmomi, wato “Mai Tsarki ga Ubangiji” a kan ƙararrawar dawakai. Tukwanen da suke Haikalin Ubangiji za su zama kamar kwanonin da suke a gaban bagade.