Zechariah 14:21 — Compare Translations
3 translations compared side by side
Hausa (Sabon Rai Don Kowa 2020)
Kowace tukunya a Urushalima da Yahuda za tă zama mai tsarki ga Ubangiji Maɗaukaki, kuma duk wanda ya zo don miƙa hadaya zai ɗauki waɗansu tukwane yă yi dahuwa da su. A ranan nan kuwa, ba Bakan’ane da zai ƙara kasance a gidan Ubangiji Maɗaukaki.
Hausa Arabic 2020 (أَتَّوْرَتْ دَ أَنَّبَاوَا)
ذَيْ كُمَ كَسَنْثٜىٰ ثٜىٰوَ كُواْوَثٜىٰ تُكُنْيَرْ دَتَكٜىٰ أَ عُرُوشَلِيمَ دَ يَهُودَ ذَاعَ كٜىٰٻٜىٰسُ دَ ڟَرْكِے غَ يَهْوٜىٰهْ مَيْ ضُنْدُنَا ؞ دُكَنْ مَاسُ مِيڧَ هَدَايَ سُطَوْكَ سُدَڢَ نَامَنْ هَدَايَ عَثِكِنْسُ؞ أَ رَانَرْ نَنْ بَذَاعَ ڧَارَ سَامُنْ مُتَنٜىٰنْ كَنْعَنَ كُواْ مَاسُ سَيَ دَ سَيَرْوَ أَ غِدَنْ يَهْوٜىٰهْ بَ؞
Hausa Bible 1979 (Littafi Mai Tsarki)
Kowace tukunya da take a Urushalima da Yahuza za ta zama tsattsarka ga Ubangiji Mai Runduna domin dukan masu miƙa hadaya su ɗauka su dafa naman hadaya a cikinsu. A wannan rana ba za a ƙara samun mai ciniki a Haikalin Ubangiji Mai Runduna ba.