Zechariah 14:4 — Compare Translations
3 translations compared side by side
Hausa (Sabon Rai Don Kowa 2020)
A ranan nan ƙafafunsa za su tsaya a kan Dutsen Zaitun, gabas da Urushalima, za a kuma tsage Dutsen Zaitun kashi biyu daga gabas zuwa yamma, yă zama babban kwari, rabin dutsen zai matsa zuwa wajen arewa, rabi kuma zai matsa zuwa wajen kudu.
Hausa Arabic 2020 (أَتَّوْرَتْ دَ أَنَّبَاوَا)
أَ رَانَرْ نَنْ ڧَڢَاڢُنْسَ ذَاسُ ڟَيَ عَكَنْ تُدُنْ ظَيْتُنْ، وَنْدَ يَكٜىٰ غَبَسْ دَ بِرْنِنْ عُرُوشَلِيمَ؞ تُدُنْ ظَيْتُنْ كُوَ ذَيْ ڟَٰغٜىٰ كَشِ بِيُ دَغَ غَبَسْ ذُوَا يَمَّ، يَبَرْ بَبَّنْ ݣُورِ أَڟَكَانِنْسُ؞ كَشِ غُدَا نَتُدُنْ ذَيْ جَنْيٜىٰ ذُوَا وَجٜىٰنْ أَرٜىٰوَ؞ كَشِ طَيَنْ كُمَ ذَيْ جَنْيٜىٰ ذُوَا كُدُ؞
Hausa Bible 1979 (Littafi Mai Tsarki)
A wannan rana ƙafafunsa za su tsaya a bisa Dutsen Zaitun wanda yake wajen gabas da Urushalima. Dutsen Zaitun zai tsage biyu daga gabas zuwa yamma, ya zama babban kwari. Sashi guda na dutsen zai janye zuwa wajen kudu. Ɗaya sashin kuma zai janye zuwa wajen arewa.