Zechariah 2:8 — Compare Translations
3 translations compared side by side
Hausa (Sabon Rai Don Kowa 2020)
Gama ga abin da Ubangiji Maɗaukaki ya ce, “Bayan ya ɗaukaka ni, ya kuma aiko ni ga ƙasashen da suka washe ku gama duk wanda ya taɓa ku ya taɓa ƙwayar idonsa ne.
Hausa Arabic 2020 (أَتَّوْرَتْ دَ أَنَّبَاوَا)
«غَمَا،» إِنْجِ يَهْوٜىٰهْ مَيْ ضُنْدُنَا ، شِ مَيْ طَوْكَكَ نٜىٰ وَنْدَ يَعَيْكٜىٰنِ، «غَا سَڧُواْنَ ذُوَاغَ أَلْعُمَّيْ، وَطَنْدَ سُكَ ڨُوثٜىٰ كَايَنْكُ؞ ‹دُكْ وَنْدَ يَتَٻَ مُتَنٜىٰنَ يَتَٻَ ڨُويَرْ عِدُواْنَنٜىٰ؞
Hausa Bible 1979 (Littafi Mai Tsarki)
Ubangiji Mai Runduna ya ce, “Bayan ɗaukaka ya aike ni zuwa wurin al'umman duniyan nan da suka washe ku, gama wanda ya taɓe ku, ya taɓi ƙwayar idona.