Zechariah 3:2 — Compare Translations
3 translations compared side by side
Hausa (Sabon Rai Don Kowa 2020)
Ubangiji ya ce wa Shaiɗan, “ Ubangiji ya tsawata maka, Shaiɗan! Ubangiji wanda ya zaɓi Urushalima, ya tsawata maka! Ashe, mutumin nan ba shi ne sandar da take ƙonewa da aka ciro daga cikin wuta ba?”
Hausa Arabic 2020 (أَتَّوْرَتْ دَ أَنَّبَاوَا)
سَيْ يَهْوٜىٰهْ يَثٜىٰ وَ شَيْطَنْ «نِے يَهْوٜىٰهْ نَا ڟَاوَتَا مَكَ، شَيْطَنْ! نِے يَهْوٜىٰهْ وَنْدَ نَذَاٻِ عُرُوشَلِيمَ تَذَمَ وُرِنْ ذَمَنَ، إِنَ ڟَاوَتَا مَكَ! وَنَّنْ يُواْشُوَ، نَكُٻُتَرْ دَشِ كَمَرْ سَنْدَنْ دَ عَكَ ڢِظْغٜىٰ دَغَ وُتَا؞»
Hausa Bible 1979 (Littafi Mai Tsarki)
Ubangiji ya ce wa Shaiɗan, “Ubangiji ya tsauta maka, kai Shaiɗan! Ubangiji wanda ya zaɓi Urushalima ya tsauta maka. Ai, wannan mutum kamar itace ne wanda aka fizge daga cikin wuta.”