Zechariah 3:9 — Compare Translations
3 translations compared side by side
Hausa (Sabon Rai Don Kowa 2020)
Dubi dutsen da na ajiye a gaban Yoshuwa! Akwai idanu bakwai a kan wannan dutse guda, zan kuma yi rubutu a kansa,’ in ji Ubangiji Maɗaukaki, ‘zan kuma kawar da zunubin ƙasan nan a rana ɗaya.
Hausa Arabic 2020 (أَتَّوْرَتْ دَ أَنَّبَاوَا)
غَاشِ نَسَا دُوڟٜىٰنَّنْ أَغَبَنْ يُواْشُوَ، دُوڟٜىٰ مَيْ غٜىٰڢٜىٰ بَݣَويْ؞› إِنْجِ يَهْوٜىٰهْ مَيْ ضُنْدُنَا ، ‹ذَنْيِ رُبُوتُو عَكَنْسَ؞ ذَنْ كُمَ طَوْكِ لَيْڢِنْ ڧَسَرْ نَنْ أَ رَانَ طَيَ؞
Hausa Bible 1979 (Littafi Mai Tsarki)
Ni Ubangiji Mai Runduna na ce, a kan dutsen da na kafa a gaban Yoshuwa, dutse mai ido bakwai zan yi rubutu, zan kawar da laifin al'umman nan rana ɗaya.