Zechariah 4:6 — Compare Translations

3 translations compared side by side

Hausa (Sabon Rai Don Kowa 2020)
Sai ya ce mini, “Wannan ce maganar Ubangiji ga Zerubbabel. ‘Ba ta wurin ƙarfi ba, ko ta wurin iko, sai dai ta wurin Ruhuna,’ in ji Ubangiji Maɗaukaki.
Hausa Arabic 2020 (أَتَّوْرَتْ دَ أَنَّبَاوَا)
سَيْ يَثٜىٰ مِنِ «غَا مَغَنَرْ يَهْوٜىٰهْ ذُوَاغَ ظٜىٰرُبَّبٜىٰلْ، ‹بَتَوُرِنْ ڧَرْڢِبَ، بَتَوُرِنْ إِيكُواْ بَ، عَمَّا تَوُرِنْ رُوحُنَ نٜىٰ،› إِنْجِ يَهْوٜىٰهْ مَيْ ضُنْدُنَا ؞
Hausa Bible 1979 (Littafi Mai Tsarki)
Sa'an nan ya ce, “Wannan ita ce maganar Ubangiji zuwa ga Zarubabel cewa, ‘Ba da ƙarfi, ko iko ba, amma da Ruhuna,’ in ji Ubangiji Mai Runduna.