Zechariah 6:10 — Compare Translations
3 translations compared side by side
Hausa (Sabon Rai Don Kowa 2020)
“Ka karɓi azurfa da zinariya daga masu zaman bauta Heldai, Tobiya, Yedahiya, waɗanda suka iso daga Babilon. A ranar kuma ka je gidan Yosiya ɗan Zefaniya.
Hausa Arabic 2020 (أَتَّوْرَتْ دَ أَنَّبَاوَا)
«كَيْ دَ كَنْكَ كَتَڢِے غِدَنْ يُواْسِيَا طَنْ زَڢَنِيَ يَوْ طِنَّنْ؞ أَوُرِنْ ذَاكَ كَرْٻِ ݣَوْتَادَغَ حَنُّنْ هٜىٰلْدَيْ دَ تُواْبِيَ دَ يٜىٰدَيَ وَطَنْدَ سُكَ إِسُواْ دَغَ بَوْتَا عَڧَسَرْ بَابِيلَ؞
Hausa Bible 1979 (Littafi Mai Tsarki)
“Ka karɓi sadaka daga Heldai, da Tobiya, da Yedaiya waɗanda suka komo daga bautar talala a Babila. A ranar kuma ka tafi gidan Yosiya ɗan Zafaniya.