Zechariah 6:7 — Compare Translations
3 translations compared side by side
Hausa (Sabon Rai Don Kowa 2020)
Da ƙarfafa dawakan suka fito, sai suka yi marmari su ratsa dukan duniya. Sai ya ce, “Ku ratsa dukan duniya!” Saboda haka suka ratsa dukan duniya.
Hausa Arabic 2020 (أَتَّوْرَتْ دَ أَنَّبَاوَا)
وَطَنَّنْ دَوَكِ مَاسُ ڧَرْڢِے سُكَ ڢِتُواْ سُنَ مَرْمَرِ سُتَڢِے دُواْمِنْ سُيِ تَكَيْوَ دَ كَٰوُاْوَ سُيِ سِنْتِرِ كُواْعِنَ عَثِكِنْ دُونِيَا؞ سَيْ مَلاَىِٕكَنْ يَثٜىٰ مُسُ «كُتَڢِے كُيِ تَكَيْوَ دَ كَٰوُاْوَ كُنَ يِنْ سِنْتِرِ كُواْعِنَ عَثِكِنْ دُونِيَا؞» سُكَ كُوَ تَڢِے سُكَيِ حَكَ؞
Hausa Bible 1979 (Littafi Mai Tsarki)
Sa'ad da ingarmun suka fita, sai suka ƙagauta su zagaya duniya don su bincike ta. Ya ce musu kuwa, “Ku tafi, ku bincike duniya, kuna kai da kawowa.” Har kuwa suka yi.